A yammacin Afirka da tsakiyar Afirka, ruwan sama ya haifar da mummunar ambaliya, musamman ma ‘yan gudun hijira da kuma mutanen da suka rasa matsugunansu. Halin da suke ciki ya yi wuya sosai, kuma suna bukatar taimako na gaggawa.
Tun da aka fara damina, ambaliyar ruwa ta yi barna sosai a kasashen Kamaru, Chadi, Mali, Nijar da Najeriya. Ana fama da ruwan sama kamar da bakin kwarya a wadannan kasashe wanda ya lalata gidaje, tituna, da ma filaye.
’Yan gudun hijirar da suka riga sun bar gidajensu saboda rikice-rikice ko bala’o’i, sun sami kansu cikin mawuyacin hali. Suna zaune a cikin matsuguni marasa ƙarfi kuma suna buƙatar abinci, ruwan sha da kula da lafiya.
Gwamnatoci da kungiyoyin agaji suna aiki tare don taimakawa, amma isa ga wuraren da ambaliyar ruwa ta mamaye galibi yana da matukar wahala. Don haka yana da mahimmanci a hanzarta yin aiki don kare mafi rauni, kamar yara.